Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matsalar Inji Ta Sa Jirgin Kasan Najeriya Tsayawa A Daji


Ana Dab Da Kamala Aikin Jirgin Kasa Daga Warri Zuwa Kogi.
Ana Dab Da Kamala Aikin Jirgin Kasa Daga Warri Zuwa Kogi.

Fasinjoji da suka taso daga tashar jirgin kasa na Rigasa da ke Kaduna zuwa Abuja sun shiga halin damuwa da rashin tabbas bayan jirgin ya lalace, ya kuma tsaya a cikin daji, sakamakon matsalar inji.

Manajan tashar jirgin kasan na NRC, Malam Aminu Ibrahim, ya tabbatar mana da aukuwar lamarin ta wayar tarho inda ya ce matsalar inji ce ta yi sanadiyar lalacewar jirgin da ya tashi da misalin karfe 7 daga ta Kaduna zuwa Abuja.

Manaja Aminu ya kara da cewa, an turo wani jirgi daga Abuja zuwa ofishin su dake yankin Loko don gyara wanda ya lalace sannan a debi fasinjojin zuwa Abuja din.

Wani fasinja da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayana cewa, jirgin safen ya sami matsalar inji ne bayan tashinsa daga tashar Rigasa da wasu yan mintuna inda ya ke tafiyar hawainiya har ya kai ga tashar kauyen Dutse, kafin daga bisani ya tsaya baki daya.

Fasinjojin da sun tsinci kan su cikin wannan yanayi na ban tsoro sakamakon matsalar ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Sun bayyana takaicinsu kan lalacewar jirgin, suna kuma nuna fargaba kan abin da kan iya biyo baya idan 'yan bindiga suka sami labarin lalacewar jirgin.

Karin bayani akan: Malam Aminu Ibrahim, Rigasa, NRC, Nigeria, da Najeriya.

Rahotannin sun bayyana cewa, wani injiniya dake zaman ma’aikacin hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya wato NRC, ya bayyana taikaicin sa da tamarin da suka tsinci kan su a ciki inda ya shaidawa fasinjojin cewa, za’a kwashe kamar sa’ao’i 2 kafin kamalla aikin gyaran jirgin.

Idan ana iya tunawa, ba wannan shi ne karon farko da jirgin kasar ke lalacewa ba, ko a cikin watan Janairun an fuskanci irin wannan matsalar lalacewar jirnin kasar sau biyu inda fasinjoji suka shafe tsakanin sa’o’i 4 zuwa 6 kafin suka isa Abuja.

Hakan kuma ya kara saka shakku a zukatan 'yan Najeriya da ke amfani da jiragen kasa don sufuri, musamman a yayin da wasu masu fashin baki suka yi zargin cewa ana sayo tsofaffin jiragen ne a maimakon sababbi, duk da yake hukumomin da lamarin ya shafa sun musanta wannan zargin.

XS
SM
MD
LG