Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Kasa: An Rufe Hanyar Abuja Zuwa Kaduna


Jirgin kasa da ke jigilar tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Najeriya
Jirgin kasa da ke jigilar tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Najeriya

Matsalar masu garkuwa da mutane da ke tare hanyar mota ta sa jama’a da dama sun koma tafiya ta jirgin kasa don gujewa fadawa tarkon masu satar mutanen.

Hukumar da ke kula sufurin jiragen kasa na Najeriya NRC ta dakatar da jigilar da jiragenta ke yi akan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Daukan wannan mataki ya biyo bayan rahotanni da suka nuna cewa an kai hari kan hanyar layin dogon da ta ratsa yankin Rijana da Duste a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Jaridun Najeriya sun ruwaito cewa Babban Darektan hukumar ta NRC Fidet Okhiria ya tabbatar da dakatar da jigilar sannan ya ce ana kan gudanar da bincike.

Hukumar ta NRC ta dora alhakin harin akan masu barnata dukiyar gwamnati yayin da wasu ke cewa ‘yan fashin daji ne.

Bayanai sun yi nuni da cewa harin wanda aka dasa abin fashewa akan hanyar jirgin, ya yi sanadin karyewar turakun jirgin ta yadda ba zai iya wucewa ba.

Gabanin hakan tsohon Sanata a jihar ta Kaduna, Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa an kai hari akan jirgin kasa da ke zirga-zirga tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Wasu hotunan da suka karade shafukan sada zumunta sun nuna yadda fashewar ta karya hanyar jirgin da kuma yadda aka kai hari kan sashen direban jirgin.

Wannan lamari ya sa ala tilas aka mayar da fasinjojin da suka taso daga Abuja zuwa inda suka fito bayan aukuwar wannan lamari.

Matsalar masu garkuwa da mutane da ke tare hanyar mota ta sa jama’a da dama sun koma tafiya ta jirgin kasa don gujewa fadawa tarkon masu satar mutanen.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kai harin kan jiragen kasa da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna ba.

XS
SM
MD
LG