Fashin Baki Kan Kisar al-Zawahiri

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa, an kashe shugaban kungiyar Al Qaeda Ayman al-Zawahiri

Tun bayan sanarwar da Amurka ta bayar jiya na kashe shugaban kungiyar Al-Qaeda, Ayman al-Zawahiri a Kabul, masu sharhi ke ci gaba da tsokaci a game da muhimmancin kisan ga fafutukar yaki da ta’addanci a duniya da kuma Amurka.

Na baya bayan nan cikin masu sharhin shi ne Mallam Mohammad Qaddam Sadiq mazaunin Dubai mai sharki kan al'amuran Gabas Ta Tsakiya, wanda Haruna ya tambaye shi yadda ya ke ganin wannan nasarar da Amurka ta samu, sai ya ce:

To bisa la’akari da muhammancin Ayman Al Zawahiri a wurin kungiyar ta Al Qa’ida ba abun mamaki ba ne da Amurka ta sanar da kisan da ta yi masa, a matsayin wata babbar nasara. Idan aka yi la’akari da irin laifuffukan da aka jingina a gare shi na cewa ya taka rawa wajen aiwatar da su - tashin bama-bamai misali da ya kashe daruruwan mutane a ofishin jakadancin Amurka da ke Tanzania a shekarar 1998, da laifin da suke ganin yana da hannu a ciki na harin da aka kai wa Amurka a New York da Washington 2001 a watan Satumba da hare-hare da aka kai a jirgin ruwa na Amurka.

Saboda haka muhimmancinsa a wajen su babba ne. Ga shi kuma ana ganin sa mutum na biyu bayan Osama Bin Ladin, kuma har akwai kyautar kudi da Amurka ta saka kan duk wanda ya bada wani bayani na sirri wanda zai iya kaiwa kai tsaye ga kama shi ko kuma a kashe shi wannan kudin ya kai dala biliyan ashirin da biyar. Saboda haka babbar nasara ce suke gani a gare su.

Ku Duba Wannan Ma Amurka Ta Kashe Shugaban Al-Qaida Ayman Al-zawahiri

Sadiq ya ci gaba da cewa: Ko da yake ita Taliban bata bada sanarwa a gwamnatance cewa Al-zawahiri ya dawo kasar Afganistan ba, amma bayanai sun nuna cewa tun bayan da Taliban ta koma mulki a Kasar Afghanistan Ayman Al- Zawahiri ya dawo kuma alamu sun nuna ya dawo ne da kariya ta hukumar ita Taliban din, idan aka yi la’akari da gidan da ya rayu a ciki, wanda an ce bai fi mita dari biyu daga gidansa zuwa gidan shugaban kasar ta Afghanistan ba, sannan kuma gida ne mallakar Ministan Harkokin Cikin Gida na gwamnatin Afghanistan ta Taliban.

Dama tabbas, musamman shugaba Biden da yake cikin tsaka mai wuya a siyasance, musamman a kasarsa ta Amurka, zai yi kokari cewa ya yi anfani da wannan nasarar da suka ci wajen wanke gwamnatinsa ko kuma kara wa gwamnatinsa yanayi na farin jini ko kuma yadawa tsakanin Amurkawa cewa lallai Amurkar tana nan akan bakarta ta bibiyar duk wadanda sukai wa Amurka laifi, kuma suke adawa da Amurka dan ganin cewa ta ga bayansu ko ta kama su, ko wani abu mai kama da haka.

Saurari cikkaken fashin bakin Qaddam Sadiq a hirarsa da Haruna Shehu:

Your browser doesn’t support HTML5

08-02-22 Fashin Baki Kan Kisar Alzawahiri