Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kashe Shugaban Al-Qaida Ayman Al-zawahiri


Shugaban kungiyar Al-Qaida Ayman Al-zawahiri.
Shugaban kungiyar Al-Qaida Ayman Al-zawahiri.

Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da cewa, an kashe shugaban kungiyar Al Qaeda Ayman al-Zawahiri a wani harin da hukumar leken asiri ta CIA ta kai a Afganistan a karshen mako, wanda shi ne tashin hankali mafi girma ga kungiyar tun bayan kashe wanda ya kafa kungiyar Osama bin Laden a shekarar 2011.

Ayman al-Zawahiri ya gaji Osama bin Laden a matsayin shugaban al-Qaida bayan shekaru da dama a matsayin babban mai shirya ta kuma mai tsara dabarunta, amma rashin kwarjininsa da gogayya daga masu fafutukar kafa daular Islama ya sa ya zabura da kai hare-hare a kasashen yamma.

An kashe Al-Zawahiri mai shekaru 71 a karshen mako a wani harin da jiragen yakin Amurka suka kai masa, kamar yadda jami'an Amurka suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin.

Al-Zawahiri ya kalli yadda al-Qaida ta yi watsi da tashe-tashen hankula sakamakon tawayen Larabawa na shekara 2010 zuwa 2011, wanda masu fafutuka da masu matsakaicin ra'ayi da masana masu adawa da mulkin kama-karya na shekaru da dama suka kaddamar.

A cikin shekaru da suka biyo bayan mutuwar bin Laden, hare-haren da Amurka ta kai ta sama sun kashe mataimakan al-Zawahiri, wanda ya raunana karfin tsageran Masar su sami damar hada kansu a duniya.

Duk da cewa al-Zawahiri ya yi suna a matsayin mutum mai sassaucin ra'ayi kuma mai fada, al-Zawahiri ya yi nasarar raya kungiyoyin da ba su da alaka da su a fadin duniya wadanda suka karu wajen kai munanan tashe-tashen hankula na cikin gida, wasu daga cikinsu sun samo asali ne daga hargitsin da ya taso daga kasashen Larabawa. Tashin hankalin ya hargitsa kasashe da dama a fadin Asiya da Afirka da kuma Gabas ta Tsakiya.

Amma kwanakin a matsayin al-Qaida na jagora, wadanda suka shirya kai wa Amurka hari a ranar 11 ga Satumba na shekarar 2001, sun dade da barin doron kasa. Don haka, tsagerancin ya koma tushensa a tashe-tashen hankula na cikin gida, lamarin da haddasa cudanya da korafe-korafe a cikin gida da kuma tunzura kungiyoyin Jihadi na kasashen duniya masu amfani da kafafen sada zumunta.

Al-Zawahiri ya kwashe shekaru masu yawa a matsayin mai kishin musulunci.

A karon farko da duniya ta ji labarinsa shi ne lokacin da ya tsaya a kejin shari'a bayan ya kashe shugaban Masar Anwar Sadat a shekarar 1981.

Al-Zawahiri dai ya shafe shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba amma aka wanke shi daga manyan laifuffuka.

XS
SM
MD
LG