Fashe-fashe da barin wuta sun jijjiga babban birnin Afghanistan

  • Ibrahim Garba

Ana cigaba da barin wuta a Siriya

‘Yan sandan Afghanistan sun ce wasu ‘yan bindiga su kaddamar da

‘Yan sandan Afghanistan sun ce wasu ‘yan bindiga su kaddamar da jerin hare-hare a babban birnin kasar da kuma akalla wani birnin kuma a Afghanistan din.

Hukumomi sun ce jerin fashe-fashe da barin wutar bindiga sun jijjiga unguwar jami’an diflomasiyya mai cike da matakan tsaro da kuma wata unguwar da ke daura da ginin Majalisar Dokoki a birnin Kabul.

Kungiyar Taliban ta dau alhakin kai jerin hare-haren, ta ce ‘yan kunar bakin wake sun auna hedikwatar NATO, da gine-ginen diflomasiyya da Majalisar Dokoki.

Shaidu sun ce ana ma iya ganin hayaki na tashi kan gine-ginen, kuma ana iya jin kararrakin jiniya a ko’ina a unguwar.

Kungiyar ta Taliban ta ce ta kuma kaddamar da hari a birnin Jalalabad da ke gabashin kasar.

Nan take dai babu bayanin makomar wadanda hare-haren su ka rutsa da su.