Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Ta Hana 'Yan Takarar Shugabancin Kasar 10 Yin Takara Ciki Har Da.....


Wakilan majalisar dokokin Masar daga banagren salafiyawa.
Wakilan majalisar dokokin Masar daga banagren salafiyawa.

Hukumar zabe ta kasar Masar ta haramatawa mutane 10 damar yin takararar shugabancin kasar, ciki harda Omar Suleiman, tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar karkashin mulkin kama kariya na Hosni Mubarak.

Hukumar zabe ta kasar Masar ta haramatawa mutane 10 damar yin takararar shugabancin kasar, ciki harda Omar Suleiman, tsohon shugaban hukumar leken asirin kasar karkashin mulkin kama kariya na Hosni Mubarak,da dan takarar daga kungiyar Muslim Brotherhood Khairat al-shater, da kuma na bangaren salifayawa Hazem Abu Isma’il.

Shugaban hukumar zaben Farouk Sultan, yaki ya bada bayanin dalilanda suka sa aka hana mutanen takara, sai dai yace suna da sa’o’I 48 su daukaka kara.

Wasu 13 sun sami amincewar hukumar, cikinsu harda tsohon babban sakataren kuhjgiyar hada kan kasashen larabawa Amr Moussa.

A karshen wata ne ake sa ran hukumar zata bayyana jerin sunayen ‘yan takarar baki daya da aka amincewa su yi takara.

Idan har aka amince da wan doka da ta haramatawa jami’an yin takara, hakan zai sake yanayin zaben kasar baki day, kuma ya janyo wani sabon rikicin siyasa mako shida kamin a fara zaben shugaban kasa da aka shirya za ayi ranar 23 da 24 na watan Mayu. Shataer da Isma’il sune wadanda ake gani suke kan gaba cikin masu takara.

XS
SM
MD
LG