Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Da Manyan Kasashen Duniya Sun Tattauna Kan Shirin Nukiliyar Kasar.


Wakilan manyan kasashen duniya da Iran a shawarwarin Nukiliya da aka yi a Istanbul.
Wakilan manyan kasashen duniya da Iran a shawarwarin Nukiliya da aka yi a Istanbul.

Asabar aka kammala tattananawa tsakanin manyan kasashen duniya da Iran gameda shirin nukiliyar kasar da ya janyo gardama tareda alkawarin sake zama a Bagadaza babban birnin kasar Iraqi ranar 23 ga watan Mayu.

Asabar aka kammala tattananawa tsakanin manyan kasashen duniya da Iran gameda shirin nukiliyar kasar da ya janyo gardama tareda alkawarin sake zama a Bagadaza babban birnin kasar Iraqi ranar 23 ga watan Mayu.

Bayan kusan sa’o’I goma ana shawarwari duka sassan biyu sunce anyi shawarwari masu ma’ana.

Babbar jakadiyarar tarayyar turai Catherine Ashton, ta bayyana shawarwarin da cewa sun gudana cikin tsari, da kuma ma'ana, ta kara da cewa taron da za a yi a Bagadaza, zai kasance ci gaba da gudanar da shawarwarin gaba gaba.

Mukaddashin mai bada shawara ga shugaban kasa kan harkokin tsaro da hanyoyin sadarwa, Ben Rhodes, shi kuma ya kira taron kyakkyawar matakin farko. Ya kira tsaida shawarwar ayi ganawa ta biyu a Bagadaza da cewa tsara ce kan gaba.

Wakilin Iran a shawarwarin Saead Jalili, ya ce taron na jiya Asabar, an samu damar tsara fahimtar juna. Yace an cimma matsaya kan batutuwa masu yawa da za a samu hadin kai da kuma amincewa kan agenda taro nag aba.

Amma in banda amincewar ko wani bangare yayi kan muhimmancin kiyaye yarjejeniyar hana yaduwar makaman atomic, da kuma yancin Iran na habaka hanyoyin samarda makamashi ta hanyoyin nukiliya, babu karin bayani kan sassa da bangarorin biyu suka cimma dai-daito.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG