Hukumar makamashin atam ta kasa da kasa, tace da kyar ta tura tawagar wakilanta zuwa kasar Korea ta arewa, domin kuwa, Korea ta arewa tace, ita kam a yanzu bata mutunta yarjejeniyar data kula da Amirka data tanadi kada tayi gwajin makamai masu linzami.
Jiya Talata da dare, mai magana da yawun hukumar Gill Tudor, ta bada wannan sanarwa. Tunda farko Korea ta arewa tayi watsi da tir din da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi, akan harba roka data yi kwanan nan, da bata yi nasarar ba.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amirka, Mark Toner yace harban rokan da Korea ta arewa tayi a ranar juma’a, wani bangare ne na mugayen halayan da take nunawa.
Jiya Talata Korea ta arewa ta lashi takobin, ci gaba da kokarin harba roka mai cin dogon zango zuwa sararin samaniya domin ta girka watan dan Adama na nazarin yanayi.