Farin Jinin Messi Na Dishewa A PSG - AP

Messi yayin da suke atisaye a PSG

Hakan na faruwa ne yayin da ake ta rade-radin dan wasan na Argentina na shirin barin kungiyar a karshen wannan kakar wasa.

Kamfanin dillancin labarai na AP, ya ruwaito cewa farin jin Lionel Messi a kungiyarsa ta Paris Saint Germain (PSG) na raguwa.

Hakan na faruwa ne yayin da ake ta rade-radin dan wasan na Argentina na shirin barin kungiyar a karshen wannan kakar wasa.

Wasu rahotanni na cewa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona zai koma.

Kafin da kuma bayan kammala wasan da PSG ta sha kaye a hannun Lyon a gida da 1-0, an ji wasu magoya bayan PSG suna masa ihu.

Wannan al’amari na faruwa ne kasa da mako guda bayan da Messi ya ci kwallaye uku.

Yayin wasan nasu da Lyon, Messi ya taka rawar a zo a gani, amma kididdiga ta nuna cewa sau 26 aka kwace kwallo a hannunsa.

A shekarar 2021, Messi ya koma PSG daga Barcelona, kungiyar da ya kwashe tsawon rayuwarsa ta kwallo yana bugawa wasa.