Lionel Messi ya ci lambar yabo ta Ballon d’Or a bangaren maza wanda ya kafa tarihin zama karo na bakwai a jere a jiya Litini, ya na mai karasa shekarar cikin burgewa, bayan kakar wasa ta karshe mai armashi da ya yi a kulub din Barcelona da kuma samun babbar lambar yabonsa ta farko ta kasa da kasa a kulub din Argentina.
Messi, dan shekaru 34, ya yi jagaba ma Argentina wajen yin galaba a gasar cin kofin Copa America a watan Yulin wannan shekarar bayan shan kayen da su ka yi a karshen manyan wasannin kasa da kasa guda hudu.
“Ina matukar farin cikin kasancewa a nan, Ina farin cikin gwagwarmayar sake cin kofina,” a cewarsa ta wajen mai masa tafinta. Ya kara da cewa, “Ban san ko shekaru nawa su ka rage ma ni ba, to amma ina fatan da yawa su ka rage. Ina son in mika godiya ta ga dukkan (tsoffin) takwarorina ‘yan wasan Barcelona da Argentina.
Messi ya tashi da maki 613, inda ya dara gwarzon dan wasan Bayern Munich kuma mai kai farmakin kwallo na Poland, Robert Lewandowski wanda ke da 580.
"Ina so in gaya wa Robert cewa abin alfahari ne zama abokin karawarsa, kuma kowa zai ce kun cancanci lashe ta a bara."
"Eh, hakika wannan kofin na musamman ne. Yana sa in ji mun cimma buri tare da tawagar 'yan wasan kasar Argentina. Hakika shekara ce ta musamman a gare ni kuma ba shakka, ya taimake ni a sabon mataki na, a wannan sabon mataki a rayuwata. Wannan komawa zuwa PSG da na yi. Kuma game da iyalina, yarana, eh, na san cewa sukan ji daɗin wadannan lokutan kuma ina jin daɗin ganin suna cikin farin ciki. Haka zalika, ina jin dadin ganin iyaye na, da kawunnai na, su ma su na murnar ganin na sake cin wannan kofin,” in ji Messi.
Mujallar kwallon kafa ta Faransa ce ke bayar da kyautar ta Ballon d’Or ga maza duk shekara, tun daga 1956 lokacin da Stanley Matthews ya lashe.
An soke lambar yabo ta 2020 saboda cutar coronavirus ta kawo tangarda ga kakar wasan.
Lewandowski mai shekaru 33 ya kafa sabon tarihin zura kwallaye a gasar Bundesliga a kakar wasa guda da cin kwallaye 41 – wato ya zarce na marigayi Gerd Müller na Jamus da daya - lokacin da ya zura kwallo a minti na karshe na wasan karshe.
Lewandowski ya ci kwallo a wasanni 19 a jere a dukkan gasa na Bayern daga Fabrairu zuwa Satumba kuma da kadan ya kasa kafa tarihin cin kwallaye a wasanni 16 na Bundesliga a jere. Gaba ɗaya dai, ya riga ya zura kwallaye 25 a wasanni 20 da ya buga wa Bayern a kakar wasa ta bana.
Kwallaye 11 da ya ci a wasanni 12 da ya buga wa Poland a bana, ya sa ya zura kwallaye 74 a wasanni 128, wanda ya gaza na Messi da guda shida kawai.
Dan wasan tsakiya na Chelsea da Italiya Jorginho ya zo na uku da maki 460 bayan ya taimaka wa kulob din na Landan lashe gasar zakarun Turai da kuma gasar cin kofin Turai. Dan wasan gaba na Real Madrid da Faransa Karim Benzema ya zo na hudu da 239.
Shi kuwa Messi ya samu kyautar Ballon d’Or biyu fiye adadin wannan kyautar da dadadden abokin gogayyarsa, Cristiano Ronaldo, ya samu, wanda shi ya zo na shida a zaben.
Kwallaye 672 da Messi ya ci wa Barcelona sun hada da gasar lig-lig na bana da ya ci kwallaye 50 a shekarar 2012; kwallaye 96 a raga a cikin 2012 da 2013; gasar Sipaniya takwas da gasar zakarun Turai shida.
A kakar wasansa ta karshe a babban kulub din na kasar Sipaniya ya zura kwallaye 38 gaba daya, inda ya lashe kofinsa na karshe tare da rawar gani a wasan karshe na Copa del Rey. A gasar Copa America, Messi ya samu kwarin gwiwa, inda ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga da kwallaye hudu sannan kuma ya taimaka aka ci kwallo biyar.
Sannan ya ba duniyar ƙwallon ƙafa mamaki ta wajen shiga kulub din Paris Saint-Germain.
Ya fara da bi a hankali ta wajen zura hudu a wasanni tara. Amma ya ci gaba da zama abin fargaba a kai a kai, ko da ba ya cikin yanayin da yake so, kamar yadda ya nuna ranar Lahadi a wasan da suka yi galaba kan Saint-Etienne da ci 3-1, inda ya yi sanadin cin dukkanin kwallaye ukun.
A wasu lambobin yabon, Kopa Trophy na mafi bajintar ɗan wasa a rukunin ‘yan kasa da shekaru 21 (under 21) , wani ɗan shekara 19 dan wasan Spain da Barcelona mai suna Pedri ne ya ci. Ya zama abin kallo a gasar Euro 2020 kuma ya kai har zuwa wasan karshe na Olympics din.
Lambar yabo ta Lev Yashin ta mafi bajintar gola, Gianluigi Donnarumma ne ya ci, wanda ya taimaka wa Italiya ta lashe gasar Euro.