Farfesa Umar Shehu Ya Rasu Yana Da Shekaru 97

Farfesa Umar Shehu

WASHINGTON, D. C. - Farfesa Umar Shehu, tsohon shugaban jami’ar Ahmadu bello da ke Zariya, da jami’ar Nijeriya ta Nasukka, ya rasu yana da shekaru 97 a duniya.

Farfesa Umar Shehu ya rasu ne da safiyar yau Litinin. Za a yi jana’izarsa a gidansa na GRA a garin Maiduguri, da karfe 5 na yammacin yau a cewar sanarwar Dandalin Dattawan Borno.