Fadar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ta tabbatar da mutuwar ta wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun mai taimakawa shugaban kasa kan harkar labaru, mallam Garba Shehu.
Sanarwar ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi jimamin rasuwar Dr. Nuhu Muhammadu Sanusi, sarkin gargajiya na birnin Dutse babban birnin jihar Jigawa.
An san shi a matsayin daya daga cikin shugabannin Arewacin Najeriya na zamani.
Kafin rasuwarsa, Sarkin ya kasance shugaban jami’ar jihar Sakkwato.
An dauke shi a matsayin jagora abin koyi a duniya, kuma yayi aiki tukuru wajen neman dauwamammen muhalli da kare muhalli, kuma mai ba da shawara kan tsiro da ciyayi da kore.
Hakazalika, tarihin rayuwar marigayi Sarkin ya nuna shi a matsayin mai ba da shawara kan rage sauye-sauyen yanayi, wanda ya sa ya gina filin wasan Golf na Dutse, da ake kyautata zaton yana daya daga cikin mafi girma a Najeriya, da ke da ciyayi na asali masu yawa da namun daji.
A cikin wata sanarwa da gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya fitar, ya jajantawa iyalai da daukacin al'ummar jihar.
Ya bayyana marigayi Sarkin, a matsayin shugaba na gaskiya kuma mutum ne mai kima a cikin al’umma, wanda aka san shi da hikima, tausayi da sadaukar da kai ga rayuwar al’ummarsa.