Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sheikh Abubakar Giro Argungu Ya Rasu


Sheikh Abubakar Giro Argungu (Hoto: Facebook/Sheikh Abdullahi Bala Lau)
Sheikh Abubakar Giro Argungu (Hoto: Facebook/Sheikh Abdullahi Bala Lau)

"Marigayin ya rasu ne bayan jinya da ya yi na dan lokaci a Birnin Kebbi."

Allah ya yi wa fitaccen Malamin addinin Islama na Najeriya Sheikh Abubakar Giro Argungu rasuwa.

Wata sanarwar da Shugaban kungiyar Jama’atul Izalatu Bid’ah wa Ikamatissunah na kasa (JIBWIS,) Sheikh Abdullahi Bala Lau ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, ta ce Sheikh Giro ya rasu ne bayan dan gajeran rashin lafiya a birnin Kebbi.

“Marigayin ya rasu ne bayan jinya da ya yi na 'dan lokaci a Birnin Kebbi. Za'a masa sallar janaza Gobe alhamis insha Allah.

“Za'a gabatar da sallar janazan Marigayi Sheikh Abubakar Giro da misalin karfe biyu na rana (2:00pm). A masallacin Idin Sarki da ke garin Argungu a jihar Kebbi, Najeriya Insha Allah.” In ji Sheikh Bala Lau.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG