Farashin Siminti Na Ci Gaba Da Hauhawa Duk Da Riban Da Kamfanonin Siminti Ke Bayyanawa

Kamfanin siminti a Nijar.

Kamfanin siminti a Nijar.

Rahotannin sun yi nuni da cewa duk da karuwa a ribar da kamfanonin sarrafa siminti ke samu a kasar, farashin siminiti na ci gaba da hauhawa cikin watanni 18 da suka gabata, lamarin da ban mamaki duk da tabbacin da masana'antun ke yi na cewa suna kara hakaka bangaren.

Tashin farashin simintin dai na haifar da hauhawar farashin saura kayayyakin gini.

Rahotannin sun yi nuni da cewa kamfanoni uku da suka hada da Dangote, Lafarge, da BUA ke kan gaba a kasuwar siminti ta Najeriya a halin yanzu kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Rahotanni sun yi nuni da cewa farashin buhun siminti mai nauyin kilogiram 50 ya fara tashi ne a cikin watan nuwambar shekarar 2020 daga naira dubu 2 da 500 zuwa dubu 3 da 600.

A halin yanzu dai, akwai gaggarumin bambanci a tsohon farashin masana'antar siminti da kuma farashin kasuwa a daidai wannan lokaci

Rahotannin dana jihar Legas sun yi nuni da cewa farashin siminti a daga kamfani a farkon shekarar nan na kan naira dubu 3 da 600 amma a yanzu har ya kai naira dubu 4.

A babban birnin tarayya Abuja, wata majiya ta bayyana cewa ana sayar da buhun simintin Dangote tsakanin Naira dubu 3 da 800 zuwa naira dubu 3 da 900 la’akari da inda wurin da ake da shi ya ke a cikin Abuja.

‘Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa a game da yanayin tsadar siminti da sauna kayayyakin masarufi inda Hajja Fanna Wakil ke cewa kamata gwamnati ta kawo wa al’umma agaji.