Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin BUA Ya Kaddamar Da Asusun Tallafawa Nahiyar Afirka Na Dala Miliyan 100


Tambarin Kamfanin Simintin BUA.
Tambarin Kamfanin Simintin BUA.

Attajirin dan kasuwa, Abdul Samad Rabiu mai kamfanin BUA ya kaddamar da wani shirin bada tallafin shekara-sheara na dala miliyan 100 na nahiyar Afirka wanda aka yiwa lakabi da “Shirin tallafin Abdul Samad Rabiu, don ci gaban zamantakewar jama'a.”

Shirin da ya kasu gida biyu, inda a kashin farko, Najeriya ce za ta amfana da kashi 50 cikin dari wato dala milyan 50, yayin da a kashi na 2 kuma sauran kasashen nahiyar Afirka zasu morewa dala miliyan 50 na shirin.

Shugaban kamfanin siminti na BUA, Abdulsamad Rabiu, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar talata yana mai cewa, shirin tallafin zai mayar da hankali kan ilimi, kiwon lafiya, da ci gaban al’umma.

Rabi'u ya ce za a fara da gina muhimman ababen more rayuwa da kuma horar da al’umma ta wadannan fanonni domin samar da ci gaba.

Shugaban Kamfanin Simintin BUA, Abdul Samad Rabiu.
Shugaban Kamfanin Simintin BUA, Abdul Samad Rabiu.

Sanarwar ta kara da cewa, manufar wannan shirin ita ce, samar da kayan aiki, neman masu bincike, likitoci, da sauran masu aiki a cikin al’umma da zimmar samar da mafita ga matsalolin da al’umma ke fuskanta tare da inganta yanayin rayuwa ga matasa.

Tallafin ASR zai kuma samawa jami’o’i 6 da ke dukannin yankunan siyasa 6 na Najeriya da za su ci gajiyar shirin na farko na Naira biliyan 1 kowannen su domin inganta yanayin karatu ta hanyar samar da gine-gine da kayan aiki a duk inda ake da gibi da bukata.

Jami’o’in da zasu ci gajiyar shirin a karo na farko sun hada da jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria, jami’ar Maiduguri, jami’ar gwamnatin Najeriya da ke Nsukka, Jami’ar Benin dake jihar Edo, Jami’ar Ilori da ke jihar Kwara da kuma Jami’ar Badun dake jihar Oyo.

Shugaban kamfanin BUA, ya kuma kara da cewa, shirin talaffin zai karkata akala kan muhimman ayyuka a tsawo wa’adin da aka tsara, kuma domin sa ido, a duk shekara za'a rika ba da rahoto a kan duk ci gaban da aka samu inda kwamitin amintattu da aka kafa zai sanya ido kan ayyuka kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Shugaban Kamfanin Simintin BUA, Abdul Samad Rabiu.
Shugaban Kamfanin Simintin BUA, Abdul Samad Rabiu.

Ya ce abu mafi mahimmanci shi ne yadda wadanda za su ci gajiyar shirin za su hada gwiwa da shirin don cimma nasarar kaddamarwa.

A cikin shekarar nan Abdul Samad Rabiu yana sa ran bayyana samar da sauran kaso 50 ga sauran kasashen Nahiyar Afirka, kuma a halin yanzu yana kan tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki da sauran abokan hulda.

Idan aka cimma matsaya kuma, kamfanin BUA zai fitar da sanarwa kan lamarin.

XS
SM
MD
LG