ABUJA, NIGERIA - A makwan jiya mazauna birane, musamman Abuja, sun sha fama da dogayen layukan fetur duk da tsananin tsadar man biyo bayan cire tallafi.
Yayin da wasu masu motoci su ka koma hawa na haya ko daka sayyada don tsananin tsadar man fetur din, farashin na zama da bambanci a gari daya daga wannan gidan man zuwa wancan.
Duk da kai tsaye fadar Aso Rock ba ta amince ko watsi da bayanan ta ba da tallafin a watan Agusta ba don hana man kara cillawa sama ba, 'yan kasuwa kan yi radin kan su, su saka farashin da za su ci riba.
Mai taimakawa shugaban Najeriya Bola Tinubu kan labaru Abdul'aziz Abdul'ziz ya ce gwamnati ta dau matakan kawo sauki duk da kuma ba za a iya kaucewa farashin gidajen man ba.
In za a tuna kungiyoyin kwadago sun janye shirin tafiya gagarumin yajin aiki bayan gwamnati ta karawa ma'aikatan taraiya albashi da Naira 35,000 tun daga watan jiya.
Babban sakataren kungiyar kwadago ta TUC Komred Nuhu Toro ya ce za su cigaba da zuba ido duk da su na ganin rashin sanin ya kamata na masu kujerun siyasa da manyan jami'an gwamnati da cire tallafin ba ya shafar rayuwar su.
Kuncin dai ya fi tsanani a arewa da ke nesa da bakin teku da hakan ya saka mai rubuta baituka Haruna Aliyu Ningi ke bukatar matasan arewa su sauya dabara "Matasan kudu ko da su na da digiri amma za ka taras za su iya shiga sana'ar sayar da ruwan leda (PURE WATER) don su na da manufar da su ke son cimmawa, amma matasan arewa kan gama karatu su tsaya jiran aikin gwamnati."
Hakika masu samun karami da matsakaicin albashi na kashe kusan mafi tsokan abun da su ke samu kan sufuri ko man fetur.
Kuma ya bayyana cewa gwamnati ta cire tallafi inda yanzu talakawa ke biyan tallafin daga aljihun su.
Saurari cikakken rahoto daga Nasiru Adamu El-Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5