Faransa Ta Kai Zagayen Wasan Karshe Bayan Doke Morocco

'Yan wasan Faransa suna murna kai zagayen wasan karshe a gasar cikin kofin duniya

Sakamakon wannan wasa na nufin Faransa za ta kara da Argentina wacce a ranar Talata ta doke Croatia da ci 3-0.

Faransa ta kai zagayen wasan karshe a gasar cin kofin duniya bayan da ta lallasa Morocco da ci 2-0.

Sakamakon wannan wasa na nufin Faransa za ta kara da Argentina wacce a ranar Talata ta doke Croatia da ci 3-0.

Dan wasan Faransa Theo Fernendez ne ya fara zura kwallo minti biyar da fara wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin kuma Randal Kolo Muani ya kara kwallo ta biyu a minti na 79.

An ga shugaban Faransa da ke filin wasan na Al Bayt a birnin Doha na kasar Qatar da ke karbar bakuncin gasar yana murna a lokacin da aka ci kwallo ta biyu.

Ita dai Argentina ta halarci gasar cin kofin duniya sau 17 inda ta kai wasan karshe sau biyar ta kuma daga kofin sau biyu a 1978 da 1986.

Faransa kuwa, ita take rike da kofin gasar, ita ma sau biyu tana daga kofin a shekarar 1998 da 2018.