Batun fara aikin matatar man Fatakwal din ya sake jawo hankulan al’umma musamman ma masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun man fetur na Najeriya ne jim kadan bayan sake jaddada yiwuwar hakan da shugaban kamfanin NNPCL, Mallam Mele Kolo Kyari, ya yi a makonnin baya-bayan nan a gaban shugaban majalisar wakilai na tarayyar kasar.
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa a yanzu sashi 1 daga cikin 15 na matatar man Fatakwal ya fara aiki wanda zai taimaka wajen kara karfin aiki ga ragowar 14.
Sai dai duk da bayani daga kamfanin NNPCL dake kara jadada cewa aiki zai fara gadan-gadan a matatar man Fatakwal, wasu masu ruwa da tsaki a fannin sun nuna rashin gamsuwa da yiwuwar hakan zuwa karshen watan Disambar da muke ciki.
A watan Yunin shekarar 2023 da muke ciki, kamfanin NNPCL ya shirya taron karawa daliban Najeriya sani a game da ayyukansa bayan komawa kamfanin kasuwanci sabanin yadda yake a da na gwamnati.
Idan ana iya tunawa a cikin watan Maris na shekarar 2019 ne aka baiwa kamfanin Tecnimont kwangila kashi na daya da ta kai Fam miliyan 38 kwatankwacin dala miliyan $50, sai kuma wani kashin kwangilar sayo kayan aikin sake gina matatar a watan Afrilun shekarara 2021 wanda ya kai fam biliyan 1.08 kwatankwacin dalar Amurka biliyan $1.5 don aiwatar da cikakken gyara ginin matatar.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5