Da yawa daga cikin kananan ‘yan kasuwa sun tabka asara mai yawa sakamakon fadiwar darajar kudin na naira.
Hakan ya fara kawo cikas cikin harkoki na ‘yan kasuwar Nijar da suke ma’amala da ita wannan naira domin saye da sayarwa a tarayyar Najeria, lamarin da ya sa al’amurran suke fuskantar koma baya ta fannoni da dama.
Matsalar fadiwar naira tafi shafar kananan ‘yan kasuwa kai tsaye inda wasu daga cikin kananan ‘yan kasuwar ke duba yiwuwar jingine kasuwancinsu har al’amurra su daidaita.
Masana tattalin arziki irin su Malam Aminou Ibrahin na jan hankalin ‘yan kasuwar da su samar da wani shirin da zasu tsira daga kariyar tattalin arziki, duba da irin tasirin da tarayyar Najeriya ke dashi a Nijar ta fuskar kasuwanci.
Sai dai yayinda yan kasuwar ke kokawa kan wannan matsalar, wasu kuma anfani suke yi da wannan damar domin zuwa sayen kayayyakin da ake samowa a tarayyar Nigeria.
A saurari cikakken rahoton Hamid Mahmoud:
Your browser doesn’t support HTML5