ABUJA, NIGERIA - Garba Chede ya yi zargin cewa akwai hannun daya daga hadiman shugaba Buhari wajen kawo cikas a rantsarwar.
Chede wanda ya ke magana a taron manema labaru, ya ce wani da bai shiga zaben ba mai suna Mubarak Bala ne ya samo nasara a kotu inda ba tare da jinkirin kammala shari’a ba, hukumar zabe ta mika ma sa shaida, yayin da kakakin majalisa ya rantsar da shi.
Chede ya ce ya garzaya kotu inda ta yanke hukuncin soke nasarar farko ta Bala har da daga bisani da umurtar ya biya duk kudin da ya karba a matsayin wakili a majalisar.
Duk da samun nasarar da tinkarar kakakin majalisa Gbajabiamila don ya ranntsar da shi, abun ya ci tura; Chede ya ce kakakin ya ce wani hadimin shugaba Buhari ne ko jami’an fadar Aso su ka hana rantsar da shi.
Ku Duba Wannan Ma Shugaba Buhari Ya Ce Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC Ya Farfado Da KimartaDa ya ke amsa tambaya ko maida martani kan dambarwar, mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya ce sam fadar ba ta da hannu a zargin.
Lauyan Chede Abdulhamid Muhammad ya ce a yanzu su na bin matakan shari’a da zai kai ga yiwuwar cafke kakakin majalisar da jefa shi gidan yari.
Saurari rahoto cikin sauti daga Nasiru Adamu El-hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5