Wannan ya hada da fafatikar da matasan kasar ke yi ta lallai sai dattawa sun ba su madafun iko, na ci gaba da jan hankalin manazarta da ke sharhi a fagen siyasar Najeriya.
A baya bayan nan dai kungiyoyin mata daban daban ne suka mamaye harabar majalisar dokokin tarayyar Najeriya domin matsa lamba ga ‘yan majalisar su shigar da wasu bukatunsu biyar cikin kundin tsarin mulkin kasa wadanda suka hada da 35% na mukaman Mulki da kuma Jam’iyyun siyasa da bada damar zama dan kasa ga bako dan kasar waje dake auren ‘yar Najeriya da kuma wajabta cewa, duk matar da ke auren dan jihar da ba jiharta ta haihuwa ba, lallai ta na da ‘yancin tsayawa zabe a jiharsa.
Sai dai manazarta na ci gaba da tsokaci akan wannan batu.
Dr Saidu Ahmad Dukawa masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero Kano ya ce inda har aka ce za a ware wa mata wasu kujeru, to matsallar ita ce, wadanne kananan hukumomi za a ware wa mata, wadanne ne na maza, kuma in har ba a sami mace da cancanta ba, ko ta ke niyyar ta tsayawa, to kenan anyi asarar kujerar kenan?
Shi kuwa a nasa bangaren, tsohon wakili a majalisar wakilan Najeriya, Hon Nasiru Garba Dantiye, bayyana ra’ayinsa ya yi akan matakin watsin da ‘yan majalisar dattawa su ka yi da bukatar shugaba Buhari ta cire sashi na 84 na dokar zabe da ke tilasta wa masu rike da mukaman siyasa yin murabus muddin za su shiga takarar zabe
Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da matasan Najeriya ke cewa, lokaci yayi da dattawan kasar ya kamata su ba su damar kama madafun ikon kasar.
Duka wadannan batutuwa na alaka ta kud da kud da shirye shiryen babban zaben Najeriya da za a yi badi wanda tuni hukumar zaben kasar ta fitar da jadawalin gudanar da shi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: