Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Osinbajo Ya Fada Ma Shugaba Buhari Aniyarsa Ta Tsayawa Takarar Shugabancin Najeriya


Farfesa Osinbajo (Facebook/Osinbajo)
Farfesa Osinbajo (Facebook/Osinbajo)

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana wa maigidansa shugaba Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a kakar zaben shekara 2023 mai karatowa, domin ya karasa aikin alkhairin da suka fara tun shekara 2015 da suka dare kan karagar mulki.

Wannan fitowa fili da Farfesa Osinbajo ya yi bai zo wa shugaba Buhari da mamaki ba, duk da cewa sai yanzu ne Osinbajo din ya bayyana aniyasara karara wa maigidansa din sakamakon yadda kafafen yada labarai suka yi ta bayyana cewa akwai yiwuwar ya tsaya neman takarar shugabancin Najeriya sakamakon kiraye-kirayen da magoya bayansa ke ta yi.

Wasu kwararan majiyoyi ne suka bayyana cewa mataimakin na shugaba Buhari ya bayyana aniyarsa ta ya gaji maigidansa din ne duk da cewa akwai yiwuwar ya fuskanci tangarda sakamakon irin jiga-jigan jam’iyyar ta APC da ke hangar kujerar ciki har da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ana iya tunawa akwa hirar da shugaba Buhari ya yi da kafafen yada labarai kuma ya sanar da cewa duk da cewa mataiamakinsa dan siyasa ne kuma lauya baya ga cewa limamin majami'a ne wato fasto bai fito fili karara ya bayyana wa al’umma wannan niyyarsa ta zama daya daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar ba da zai gaje shi Buhari, kungiyoyi da daidaikun mutane na nuna bukatar su na ya kasance daya daga cikin 'yan takarar jam’iyyarsu ta APC.

A baya-bayan nan ma sai da wasu kungiyoyi kamar su Citizen Unite wato hada kan ‘yan kasa suna ta amfani da kafafen yada labarai ciki har da na sada zumunta wajen kira ga farfesa Osinbajo da ya amsa kiransu na ya fito a kara da shi wajen takarar shugabancin kasar a shekarar 2023 mai zuwa.

Idan ana bibiyar kalmomin shugaba Buhari tun da aka fara yada jita-jitar Osinbajo zai tsaya takarar shugabancin kasar bayan wa’adin mulkinsu tare ya kare, shugaban na taka-tsantsan da kalamansa inda ya sa albarka a bisa niyyar mataimakin nasa kamar yadda ya sa albarka a niyyar jigon jam’iyyar ApC Bola Tinubu a lokacin da shi Tinubun ya kai masa ziyara kuma ya gaya masa niyyarsa ta gadar kujerarsa shi ma.

Idan ana bibiyar yadda abubuwa ke tafe a jam’iyyar APC akwai jiga-jigai da dama masu hankoron gadon wannan kujerar ta shugabancin Najeriya.

Cikin wadanda suke wannan hankoron akwai tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Imo, sanata Rochas Okorocha, Sanata Orji Uzo Kalu da ke zaman tsohon gwamnan jihar Abia da dai sauransu duk sun fito da aniyarsu ta neman yin takarar shugabancin kasar.

Baya ga wadannan tsoffin gwamnoni, ana rade-radin cewa akwai mutane daga arewacin Najeriya da a nan gaba za su fito fili da niyyarsu ta shiga jerin wadanda za su tsaya neman wannan muhimmiyar kujerar ta shugabancin kasar mai mutane sama da miliyan 200.

Masana siyasa dai na ganin cewa mataimakin na shugaba Buhari zai iya fuskantar tangarda a bisa niyyarsa, musamman wajen samun tikitin shiga babban zaben daga jam’iyyarsa ta APC saboda daga bangaren kudu maso yamma akwai Bola Ahmed Tinubu wanda a baya farfesa Osinbajo ya masa kwamishina lokacin da yake gwamnan jihar Legas, kuma shi ya zabe shi a matsayin mataimakin shugaba Buhari wanda ake ganin zai sa lamarin ya zama mai wuya a wajensa ya wuce wannan matakai.

Haka kuma, akwai rade radin cewa cikin masu hangar wannan kujera mafi mahimmanci a Najeriya, akwai ministan sufuri Rotimi Ameachi, shugaban babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti da kuma ministan kwadago Chris Ngige wadanda a nan gaba kadan za su fito da aniyarsu ta neman tikitin jam’iyyar APC wajen ganin sun sami mulkin kasar.

Rahotannin sun yi nuni da cewa mataimakin shugaba Buharin ya na shirin ganawa da shuwagabannin jam’iyyar APC a matakin jihohi da yammacin yau Litinin saidai an dage taron kuma wasu daga cikin shuwagabannin jam’iyyar suna birnin Abuja a lokacin da labarin dage taron ya riske su.

Wasu 'yan siyasa dai sun bayyana cewa ana sa ran a wannan taron ne Osinbajo zai yi amfani da damar da zai samu wajen bayyana musu aniyarsa ta fitowa takarar da neman goyon bayansu da hadin kai wajen ci gaban kasa,

A wani bangaren kuwa, wasu mambobin jam’iyyar APC na rade-radin cewa zai yi amfani da damar taron ne don sulhuntu 'yan jam’iyya a bisa matsalolin cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG