WASHINGTON D.C —
Kamfanin Facebook ya bayyana cewa ya dakatar da manhajoji dari biyu wanda ya ke gudanar da bincike su.
Facebook, ya ce a ranar litinin ya dakatar da manhajoji dari biyu da ya ce yana da alamar tambaya akan su kuma ya fara gudanar da bincike akan su a sakamakon badakalar Cambridge Analytica wanda ake zaregi ya yi amfani da su wajan nadar bayanan mutane a loakcin zaben shuagab kasar Amurka.
Mujallar Express ta wallafa cewa kafanin ya ce zai yiwa wadannan manhajoji cikakken bincike.