A yau Talata ne Emmanuel Emenike ya fitar da sanarwar zai yi murabus daga bugawa kasar sa wasa, bayan da kasa jefa kwallo raga a wasan Najeriya na kwana kwanan nan.
‘Dan wasan mai shekaru 28 da haihuwa ya kafe a shafinsa na Instagram, yana bayyanawa magoya bayansa cewa ya kawo karshen shekaru 5 da yayi yana bugawa kasarsa wasa, inda yace “daga yanzu bana daga cikin tawagar Super Eagles”
Ya dai ci gaba da cewa ina mai matukar farin ciki da wasa da samun nasara tare da tawagar mu.
“Ina mai alfahari da nasarorin da na samu a shekaru biyar din da na kwashe ina bugawa kasata wasa, na yanke shawarar na hakura haka domin kaucewa duk wani abinda ka iya zuwa.”
Emenike dai ‘dan wasane da yake bugawa kungiyar nan ta Dubai mai suna Al Ain wasa, kuma shine ‘dan wasa na biyu da yayi murabus daga bugawa Super Eagles wasa a cikin wannan watan.
Shima mai tsaron gida na kungiyar Super Eagles Vincent Enyeama, ya yi murabus bayan da suka samu rashin jituwa da babban kocin Najeriya Sunday Oliseh.