Cristiano Ronaldo ‘dan wasan kungiyar Real Madrid ya karbi lambar yabo ta ‘dan wasan da yafi kowa zura kwallo a raga ta Golden Shoe Award, ranar Talata bayan jefa kwallaye 48 a kakar wasan shekara ta 2014 zuwa ta 2015 kuma wannan shine karo na hudu da ya lashe gasar.
Ana bayar da wannan lambar yabon ce dai ga ‘dan wasan Turai da yafi zura kwallaye, amma Ronaldo ‘dan asalin Portugal ya buge takwaransa Lionel Messi, wanda yake ya zura kwallaye 43 a gasar.
Alokacin da yake karbar kyautar tare da iyalansa Ronaldo, yace “ban taba mafarkin lashe gasar har sau hudu ba, sau daya ko sau biyu amma ba sau hudu ba.”
Ronaldo dai ya taba samun wannan kyautar sau ‘daya a kungiyar Manchester United, ya kuma kara samun ta har sau biyu da Real Madrid.
Kwana kwanan nan ne aka girmama ‘dan wasan mai shekaru 30 da haihuwa bayan da ya wuce Ra’ul, a matsayin wanda yafi kowa jefa kwallo a wasan La Liga.