WASHINGTON DC - Babbar Kotun Jihar Legas dake zamanta a Ikeja ta jinkirta yanke hukunci har sai nan gaba game da karar da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya shigar yana kalubalantar huruminta na sauraron shari’arsa akan tuhume-tuhumen Da Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya ke yi masa.
Ta hannun lauyansa kuma Babban Lauyan Najeriya, Olalekan-Ojo, Emefiele ya bayyana cewar babu wata babbar kotun jiha dake da hurumin yi masa shari’a a bisa tuhumar cin amanar mukami saboda hakan zai bijiro da batutuwan tanade-tanaden kundin tsarin mulki dana shari’a.
Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriyar ya kara da cewar tuhuma ta 1 zuwa ta 4 daga cikin tuhume-tuhume 26 da Hukumar efcc ke yi masa sun sabawa kundin tsarin mulki kuma basa cikin dokokin najeriya.
Saidai EFCC ta bakin lauyanta wanda shima Babban Lauyan Najeriya ne, Rotimi Oyedepo ta kalubalanci hujjojin.
Ta hanyar kafa hujja ta hukunce-hukuncen da Kotun Kolin Najeriya ta yanke, Oyedepo ya bukaci alkalin kotun, Mai Shari’a Rahman Oshodi, da kada ya jinkirta ko dakatar da shari’ar a bisa la’akari da kalubalantar wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake magana akai.