Tuni dai Emefiele ke fuskantar tuhumar zamba a wata kotu a Abuja babban birnin kasar - wanda ya musanta - bayan tsare shi a watan Yunin bara da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta yi. Daga baya aka mayar da shi hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, kuma an bayar da belinsa a watan Nuwamba.
Tuhume-tuhumen na baya-bayan nan sun hada da karbar cin hanci, karbar kyaututtuka, da aikata almundahana, da mallakar dukiyoyin gidaje ta hanyar rashin gaskiya, da samar da wasu damarmaki ma abokansa wadanda ba su cancanci samu ba, kamar yadda takardun kotu su ka nuna.
Da aka tuntubi wani mai wakiltar Emefiele wajen shari’ar bai amsa bukatar jin ta bakinsa ba kan sabbin tuhume-tuhumen da aka yi masa ranar Asabar.
A ranar 9 ga watan Yuni ne dai shugaba Bola Tinubu ya dakatar da tsohon gwamnan babban bankin kasar, sannan aka kama shi kwana guda bayan hakan. Ya yi murabus ne a watan Agusta, inda ya share fagen nada sabon gwamna Olayemi Cardoso a watan Satumba.
A ranar Juma’a wani mai bincike na musamman da shugaba Tinubu ya dauka domin ya binciki babban bankin kasa karkashin Emefiele ya ce ya kammala aikinsa. Ba a bayyana rahoton nasa ba.
Dandalin Mu Tattauna