El Rufai Ya Tura Wakilai Taron Sasanta Rikicinsa Da NLC

Taron sulhu tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar kwadago ta NLC

Muryar Amurka ta tabbatar da halartar tawagar wakilan gwamnatin jihar, wacce ta samu jagorancin kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Ja’afaru Sani.

Rahotanni da muka samu daga Abuja, babban birnin Najeriya, na nuni da cewa, gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta tura wakilanta zuwa taron sasanta takaddamar da ke tsakaninta da kungiyar kwadago.

Gabanin wannan zaman, Gwamna Malam Nasiru El Rufai ya ce gwamnatinsa ba za ta halarci taron ba yayin da babu wutar lantarki a jihar wacce aka katse sanadiyyar yajin aikin da aka shiga.

Wakilin Jihar Kaduna, Kwamishinan kananan hukumomi Jaafaru Sani

Muryar Amurka ta tabbatar da halartar tawagar wakilan gwamnatin jihar, wacce ta samu jagorancin kwamishinan kananan hukumomi, Alhaji Ja’afaru Sani.

El Rufai da kungiyar ta kwadago ta kasa NLC, sun yi ta kai ruwa rana bayan da NLC ta kaddamar da yajin aikin kwana biyar a ranar Litinin a matsayin gargadi.

Boren ya biyo bayan sallamar dubban ma’aikata da gwammatin jihar ta yi, abin da NLC ta ce ba a yi adalci ba.

Shugaban NLC, Ayuba Wabba, a wajen taron

Yajin aikin, wanda aka yi na kwana uku, ya durkusar da al’amuran yau da kullum a jihar, inda bankuna, ma’aikatu da da tashar tashin jirage suka rufe kofofinsu.

Har ta kai ga ma’aikatan hukumar samar da wutar lantarki sun katse ayyukansu, lamarin da ya jefa daukacin jihar cikin duhu har tsawon kwana ukun da aka kwashe ana yajin aiki.

Chris Ngige, a wajen taron sulhun

Gwamna El Rufai ya zargi shugaban kungiyar kwadago Ayuba Wabba da mukarrabansa da yunkurin kassara tattalin arzikin kasar, lamarin da ya sa ya ayyana cewa yana neman Wabba ruwa a jallo.

Sai dai kamara yadda rahotanni suka nuna, gwamnan da Wabba sun yi arba da juna yayin da kungiyra ta NLC ke zanga zanga, amma babu wanda ya kama shi.

Kungiyar ta NLC ta janye yajin aikin, bayan da Ministan Kwadago Chris Ngige ya ya shiga tsakani, ya kuma gayyaci bangarorin biyu teburin sasantawa a Abuja, wanda aka gudanar a ranar Alhamis.