Tsohon dan wasan kwallon Kafa na kasar Senegal wanda ya fafata a kungiyoyin kwallon Kafa irinsu Liverpool, Bolton, Sunderland, Blackburn, da Leed United, duka a kasar Ingila El Hadji Diouf, na sha'awar shiga siyasa don tsayawa takaranr shugaban kasa a kasar sa ta Senegal.
El Hadji Diouf 37 wanda ya shafe shekaru sama da12 yana taka leda a yankin nahiyar Turai ya ce ya yanke shawarar shiga hidimarne don yin siyasa saboda yana da mutane kuna suna jiran ya canza abubuwa a ƙasar kuma y ace yana shirye ya yi hakan domin yana so ya zama jagora na matasan kasar ta Senegal.
kwararren tsohon dan wasan Chelsea da Paris Saint-Germain Gorge Weah, ya zama zabeben shugaban kasa na kasar laberiya amman kafin nan sai da ya zamo dan majalisar dattawa, kuma ba shine karo na farko da Weah, ya tsaya takaraba kafin ya samu nasara.
Your browser doesn’t support HTML5