Eguavoen Ya Ajiye Aiki, NFF Ta Rusa Tawagar Masu Horar Da Super Eagles

Augustine Eguavoen

Tuni hukumar kwallon kafar kasar ta NFF ta janye kwantiragin shekara biyu da rabi da ta ba Eguavoen, kana ta rusa tawagar masu horar da kungiyar ta Super Eagles.

Rahotanni daga Najeriya na cewa kocin Super Eagles Augustine Eguavoen, ya ajiye aikin na horar da ‘yan wasan kwallon kafar kasar.

Hakan ya biyo bayan kaye da Najeriya ta sha a hannun ‘yan wasan Black Stars na Ghana a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Najeriya ta gaza samun gurbin ne bayan da ta tashi 0-0 a filin wasa na Baba Yara da ke Kumasi a ranar Juama’a.

Sannan suka yi kunnen doki da ci 1-1 a Abuja a ranar Talata, lamarin da ya ba Ghanar damar doke Super Eagles saboda kwallo da ta ci a gidan Najeriya.

Tuni hukumar kwallon kafar kasar ta NFF ta janye kwantiragin shekara biyu da rabi da ta ba Eguavoen, kana ta rusa tawagar masu horar da kungiyar ta Super Eagles.

“Za a sanar da wata sabuwar tawagar gudanar da kungiyar bayan an yi kwakkwaran nazari don a kara farfado da kungiyar ta Super Eagles domin ta fuskanci kalubalen da ke gabanta.” Wata sanarwa da NFF ta fitar ta ce kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito a ranar Alhamis.