Cikin manyan mutanen da hukumar EFCC zata gayyato sun hada da tsohon shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar PDP Chief Tony Anenih da tsohon mai bada shawara ga shugaba Shehu Sahagari Tanko Yakasai da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Chief Olu Falae da tsohon gwamnan jihar Oyo Abdulrashid Ladoja.
A firarsa da Muryar Amurka Tanko Yakasai yace abun da ake yi a ksar ya sabawa shari'a.Yace an kama Dasuki amma har zuwa yanzu ba'a shigar da kara akan laifin da ake zarginsa da yi ba.
Akan ko zasu mayar da kudin da aka ce sun karba yace sai sun je kotu tukunna. Yace akwai mutane takwas ko tara da aka baiwa miliyan dari dari amma shi kwamitinsu aka ba kudin.
To saidai a wani halin kuma Kanar Jafaru Isa ya mayarda kashi sittin cikin kudin da aka ce ya karba tare da yin alkawarin biyan sauran nan ba da dadewa ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5