Kungiyar dalibai Musulmi a Najeriya (MSS a takaice) ta ce za ta shiga yaki da da tsattsauran ra’ayi gadan-gadan ta wajen sa ido kan dalibai Musulmi ‘yan Najeriya da ke kasashen waje – musamman wadanda ke kasashen larabawa. Ta ce daukar wannan matakin ya zama dole ganin yadda ake ta cusa ma daliban tsauraran ra’ayoyi yayin da su ke dalibta a irin wadannan kasashen.
Shugaban kungiyar na Najeriya baki daya, Alhaji Muhammad Jameel Muhammad, ya fada a wani taron kaddamar da shirin koyar da sana’o’i da ilimin zamantakewa da kungiyar ta shirya a Minna, fadar gwanatin jahar Naija, cewa tuni ma kungiyar ta shiga hada gwiwa da wasu takwarorinta na kasashen waje.
Malam Jameel y ace a shekarar da ake gab da shiga za a yi wani gawurtaccen taron kungiyoyin Musulmi na Afirka baki daya a garin Sakkwaton Najeriya, inda za a kara jaddada hakan kamar yadda aka yi a baya. Y ace har Amurka ma za su je don ganawa da sauran Musulmi dalibai.
Ga wakilinmu a Minna Mustafa Nasiru Batsari da cikakken rahoton: