EFCC Zata Cafke Wasu Tsofin Gwamnonin

Hukumar EFCC

Hukumar EFCC, tace wasu tsofin Gwamnonin da dama na cikin jerin wadanda zatayi awon gaba dasu, kakakin hukumar Wilson owodiran na nuni da cewa bazai bayana sunayen Gwamnonin ba wanda zai kasance tafkar riga Malam Masalaci ne.

Amma ya nanata cewa bawai suna gayyata ko kama wadanda suke tuhuma da almundahana dan su burge shugaba Buhari bane, ya bar shugaban hukumar na yanzu Ibrahim Lamurde, bisa mukamisa.

Ya kara da cewa “ Mu dai muna aikin ne bisa ka’idar da doka ta shinfida,”

Har zuwa farkon makon nan tsohon Gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako da dansa Sanata Abdulazeez, na ci gaba da kasancewa a tsare duk da samu beli daga alkali E.S Chukwu, na babban kotun tarayya Abuja, kan yarjejeniyar beli, Naira milyan dari ukku da hamsin.

Sanata Abdulazeez dai na ganin cewa sun shiga samu tsangwama ne bawai don batun almundahana na Naira biliyan arba’in ba amma tun lokaci da mahaifisu ya rubuta wasikar zargin tsohowar Gwamnatin Jonathan, da halin ko in kula kan Boko Haram.