Muryar Amurka ta tambayi kakakin hukumar ta EFCC Mr. Wilson Uwajeren ko gaskiya ne hukumar ta soma cafke manyan tsoffin jami'an tsaro bisa ga zargin cewa suna da hannu a badakalar karkata kudaden sayen makamai zuwa aljihunsu.
Kakakin ya tabbatar cewa da gaske ne sun kama wasu amma yace shi bai san yawan wadanda suka riga suka shiga hannunsu ba. Ya kara da cewa ana nan ana gudanar da bincike.
Air Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa tsohon sojan saman Najeriya yace su tsoffin manyan sojojin babu abun da suka sa a gabansu illa su debi dukiyar jama'a su sa a aljihunsu suna anfani dasu ta wata hanya tare da shata karya cewa an sayo makaman.. Yayi misali da inda shi ya yi aiki yace akwai wasu kwangiloli da aka bayar za'a sayo wasu jiragen yaki amma sai wasu da aka kawo cikin akwatuna da ba'a yi komi dasu ba. Haka aka zauna aka kwashi kudin mutane aka tafi dasu.
Ita ma hedkwatar tsaron Najeriya ta damke wasu tsoffin manyan hafsoshi. Amma daraktan watsa labarai na hedkwatar Kanar Rabe Abubakar ya ki ya tabbatar da labarin.
A wani halin kuma wata majiya tace tsoffin janar-janar sun yi tayin maida wasu kudade da suka wawure.
Dr Bawa Abdullahi Wase mai sharhi akan harkokin tsaro yace abu mafi a'ala yanzu shi ne a dawo da kudin amma kuma su saurari hukunci.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5