Ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro ya kafa kwamitin da ya kunshi mutane 13 domin ya binciki yadda aka kashe kudaden da aka tanada na sayowa jami'an tsaro kayan aiki tun daga shekarar 2007 zuwa 2015.
Kodayake kwamitin bai kammala aikinsa ba ya yi shimfida da wani rahoto na wucin gadi wanda ya mikawa shugaban kasa. Shi wannan takaitaccen rahoton ya bankado irin badakalar da aka yi da yadda aka yi watanda da kudaden jama'a.
Kawo yanzu kwamitin ya gano cewa ba tare da bin ka'ida ba aka kashe makudan biliyoyin nera da suka kai N643,817,955,885.18 yawanci akan karya. Banda Nera da aka kashe akwai dalar Amurka fiye da biliyan biyu ko $2,193,815,000.83 da suma suka bi iska.
Kudaden ma da gwamnonin jihohi suka tara da wadanda 'yansandan kasar da 'yansandan fararen kaya wato SSS suka tara basa cikin lissafi. Amma abun mamaki shi ne abun da aka yi anfani dashi aka sayawa jami'an tsaro kayan aiki kalilan bai taka kara ya karya ba.
Kwamitin ya gano an bada kwangololi na biliyoyin nera da dala, an biya kudaden amma ba'a yi aikin ba. Kudaden da aka kashe akan kwangilolin bogi sun wuce dala biliyan daya da majalisun dokokin kasar suka amince wa Shugaba Jonathan ya ciwo bashinsu daga kasar waje domin a yaki Boko Haram a arewa maso gabas.
Kwamitin ya bankado wata badakalar da mai ba shugaba Jonathan shawara akan harkokin tsaro , Sambo Dasuki ya yi. Shi kadai ba tare da izinin kowa ba ya biya wani kamfani N3,850,000,000.00. Ko takardun shaidar bashi gwangila ko aikin da kamfaninya yi babu. Ya yi gaban kansa ne kawai.
Bugu da kari tsakanin watan Maris na shekarar 2012 da Maris na shekarar 2015 Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ya bada wasu kwangilolin bogi har guda uku. Akwai ta N2,219,188.609.50. Akwai ta dalar Amurka $1, 671, 742, 613.58 da kuma ta Euro 9, 905, 477.00. Ya bada kwangilolin ne da sunan sayan jirage sama masu saukan angulu 12 da bamabamai da wasu kayan yaki. Dukansu babu wanda aka saya. Haka aka bar mayakan sama babu kayan aiki.
Abun da kuma ya fi daukan hankalin mutum shi ne yadda aka ba kamfanoni biyu kwangilaolin N350,000,000.00 da $1,661, 670, 469.71 da Euro 9, 905, 477.00. Wadannan kamfanonin sun yi kamarin suna wajen kin gudanar da ayyukan da aka basu amma kuma duk da haka aka biyasu makudan kudade akan abun da basu yi ba.
Kanar Sambo Dasuki ya kuma ba babban bankin Najeriya umurnin ya aika da dalar Amurka $132, 050, 386.97 da Euro 9, 905, 473.55 zuwa wasu asusun dake wasu bankuna a Ingila da Amurka ba tare da bada wani dalili ba ko takardun kwangila ko kuma wani bayani.
Saboda abubuwan da aka bankado Shugaba Buhari ya bada umurnin a kama duk wadanda suke da hannu a wadannan muna-munan da kamfanonin da aka ayana sunayensu a rahoton.