Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dasuki: Kotu Ta Dage Kara Zuwa Nuwamba 23


FILE - Nigeria's National Security Adviser Mohammed Sambo Dasuki listens to a question after his address at Chatham House in London, Jan. 22, 2015.
FILE - Nigeria's National Security Adviser Mohammed Sambo Dasuki listens to a question after his address at Chatham House in London, Jan. 22, 2015.

A yau Litinin wata kotun gwamnatin tarayya ta dage karar da tsohon mai baiwa shugaba shawara a fannin tsaro, Kanar Sambo Dasuki kan kawanyar da hukumar tsaron farin kaya ta SSS ta yi ma gidansa.

Ana dage karar ce zuwa 23 ga watan Nuwamba bayan da alkalin kotun Justice Adeniyi Ademola ya amince bangaren gwamnati ta kammala kintsawa, bukatar da lauyoyin Dasuki suka amince.

A ranar juma’ar da ta gabata ne kotu ta ba da umurni hukumar farin kayan ta SSS da ta janye daga gidan Sambo domin ya fita zuwa kasar waje neman magani.

Sai dai rahotanni sun ce hukumar ta yi biris da wannan umurni da kotun ta ba ta, koda ya ke lauyansu ya musanta.

Ana dai zargin Dasuki ne da mallakar makamai da kuma zargin cewa ya karkata akalar kudaden da aka ware domin sayan makaman da za a yaki Boko Haram.

Dasuki ya garzaya zuwa kotu domin neman a kawo karshen daurin talalar da ake mai a gidansa da ke Abuja.

Kanar Dasuki mai ritaya ya kasance shi ne mai baiwa tsohon shugaban kasar shawara kan harkar tsaro, wato Goodluck Jonathan.

Sharhi Kan Kawanyar Gidan Sambo Dasuki

Yanzu haka masana harkar shari’a a Najeriya na ci gaba tofa albarkacin bakinsu dangane da tsare Dasuki da kuma bijirewar da hukumar tsaro ta farin kaya ta yi ga umurnin kotu.

Kuma tun bayan wannan kawanya har ila yau ake ta cecekuce game da wannan batu a Najeriya.

Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu Elhikaya ya tattauna da masanin shari’a, Barrister Modibbo Bakari wanda ya yi sharhi kan lamari kamar yadda za ku ji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG