Hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya ta’annati (EFCC) ta bukaci a dage sauraron sabuwar shari’ar da ake yiwa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello, inda tace har yanzu wa’adin kwanaki 30 na tsohon sammacin da aka bashi basu cika ba.
EFCC ta kuma bada belin mutanen da ake tuhuma tare da tsohon gwamnan Jihar Kogin, Umar Oricha da Abdulsalami Hudu tare da bukatar kotun ta tsawaitawa Yahya Bello lokacin gurfana a gabanta.
A yayin zaman kotun gaban mai Shari’a Maryam Anenih ta babbar kotun tarayya ta birnin tarayya, Abuja, lauyan EFCC Jamiu Agoro ya bayyana cewa har yanzu umarnin da kotun ta bayar a ranar 3 ga watan Oktoban da ya gabata bai daina aiki ba.
“A bisa wannan dalili, muna ganin bai dace mu cigaba da sauraron karar alhali wa’adin kwanaki 30 din bai cika ba. Don haka mun tattauna tare da amincewa mu sake dawowa a ranar 27 ga watan Nuwambar da muke ciki,” kamar yadda ya shaidawa kotun.
Ya kuma kara da cewa ranar da aka tsayar a baya ta 20 ga watan Nuwamba bata yiwa bangaren masu kara daidai ba.
Daga nan Mai Shari’a Anenih ta dage zaman kotun zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba domin gurfanar da wadanda ake tuhuma.