Hukumar EFCC ta tabbatar da fara aikin bincike a kan lamarin, inda ta ce a yanzu ta tura takardar gayyata ga tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi da wasu mutane don neman bahasi daga gare su.
Takardun pandora dai su ne mafi yawan takardu da aka bankado tare da hadin gwiwar yan jaridu a duniya da adadinsu ya kai miliyan 11.9 wadanda suka fito da bayanan sirri kan asusun manyan shuwagabannin duniya musamman harkokinsu na gabar teku wato kudaden da suke boyewa don gujewa biyan haraji.
A cikin takardun da aka bankado na asusun kudadden jiga-jigai a duniya, akwai sunayen tsaffi da shugabannin duniya da ke kan karagar mulki 35, sama da yan siyasa 330 ciki har da yan Najeriya, da wasu jami’an gwamnati daga kasashe da yankuna 91 na duniya.
Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Abdulrasheed Bawa, ya tabbatar da gayyatar Peter Obi zuwa hukumar domin amsa wasu tambayoyi.
Masana shari’a dai na alakanta gayyatar Peter Obi da rashin bayyana dukkan kadarorin da ya mallaka na ciki da wajen kasar ga kotun da'ar ma'aikata wato code of conduct tribunal a lokacin da ya ke gwamna.
A yayin mayar da martani ta bakin kakakinsa, Valentine Obienyem, a cikin wata sanarwa game da gayyatar sa da EFCC ta yi a ranar litinin don ya bayyana a ofishinta a ranar 27 ga watan Oktoba da mu ke ciki, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, ya ce zai mutunta takardar gayyatar EFCC da zarar an kawo masa, ya na mai cewa akwai yiyuwar an tura wasikar zuwa wani tsohon adireshin ofishinsa ne shi ya sa ba’a kai gareshi ba.
Baya ga Peter Obi, an ambaci sunayen babban daraktar hukumar NPA, Mohammed Bello-Koko, sanata Stella Oduah, gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi, takwararsa na jihar Osun, Gboyega Oyetola, tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu, gwamna Dapo Abiodun da dai sauransu.
Domin karin bayani saurari rahotan Halima Abdurra’uf.
Your browser doesn’t support HTML5