Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitaccen Tarihin Colin Powell


Marigayi Colin Powell
Marigayi Colin Powell

Janar Colin Powell, wanda shi ne bakar fata na farko da ya rike mukamin Sakataren harkokin wajen Amurka ya mutu ne a ranar Litinin bayan fama da cutar COVID-19. Shekarunsa 84.

- An haifi Colin Luther Powell a birnin New York a ranar 5 ga wata Afrilun 1937

- Ya kasance wanda aka dama da shi a fannonin siyasa da diflomasiyya kuma Janar din soja ne mai anini hudu.

- Shi ne Sakataren harkokin wajen Amurka na 65 inda ya rike mukamin daga 2001 zuwa 2005

- Shi ne bakar fata (Ba’amurke dan asalin Afirka) na farko da ya rike mukamin Sakataren harkokin wajen Amurka.

- Shi ne mai ba da shawara kan tsaron kasa na 16 inda ya rike mukamin daga 1987 zuwa 1989.

- Ya kuma taba rike mukamin shugaban gamayyar hafsan hafsoshin sojin Amurka daga 1989 zuwa 1993.

- Ya yi karatunsa a fannin ilimin nazarin yanayi kasa inda ya kamala da babbar daraja a Kwalejin New York ta CCNY

- Ya kwashe shekara 35 yana aikin soja inda har ya kai mukamin Janar mai anini hudu.

- A shekarar 1989 ya zama Kwamanda a rundunar sojin Amurka

- Ya samu lambobin yabo da dama a Amurka da kuma wajen Amurka inda dakarun wasu kasashe suka karrama shi.

- A shekarar 2008, ya ki bin sahun jam’iyyarsa ta Republican, inda ya marawa Barack Obama baya wanda ya zama bakar fata na farko da ya shugabanci Amurka.

- A watan Satumbar shekarar 2005, Powell ya amsa cewa jawabin da ya yi a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya kai ga mamayar da Amurka ta yi wa Iraqi, yana cike da kurakuran da suka samo asali daga bayanan sirrin da aka tattara.

XS
SM
MD
LG