EFCC Ta Gargadi Masu Sana’ar POS Kan Sanin Ka’idojin Mu’amula Da Kudade

ABUJA: Sabon ginin EFCC

ABUJA: Sabon ginin EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta gargadi masu mu’amula da kudade ta na’urar POS, akan su kiyaye ka’idojin mu’amula da kudade ko su dandana kudarsu.

Yaki da almundahanar kudade da gwamnatin Najeriya ke yi sau da yawa yakan samu cikas sanadiyar mayaudara dake hulda da masu sana'ar hada-hadar kudi ta amfani da na'urar POS.

A cewar shugaban hukumar EFCC jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara, Bawa Usman Kaltungo, hakan na faruwa ne saboda karancin ilimi na dokokin hada-hadar kudade ga masu sana'ar.

Karin bayani akan: EFCC, Abubakar Atiku, Sokoto, Nigeria, da Najeriya.

Wannan a cewar sa matsala ce wadda ba ruwan doka idan aka samu masu wannan sana'ar suka yi ba daidai ba to doka zata yi aikin ta akan su.

Su kansu masu wannan sana'ar sun ce lallai sau da yawa sukan hadu da matsaloli sanadiyar ‘yan damfara, kamar yadda Abubakar Atiku ya shaidawa sashen Hausa, wanda shima jagora ne ga masu wannan sana'ar.

Masanin tattalin arziki Bashir Muhammad Achida na jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto, ya ce bisa la'akari da yadda sana'ar ta POS ke bunkasa da kuma yadda mayaudara suka yi yawa akwai bukatar masu sana'ar su san dokoki mu’amula da kudade.

Bisa la'akari da yadda hada-hadar kudade ta amfani da POS ke yawaita a Najeriya, akwai yuwuwar idan ba a yin taka tsan-tsan masu wannan sana'ar kan iya fadawa tarkon mayaudara.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

Your browser doesn’t support HTML5

EFCC Ta Gargadi Masu Sana’ar POS Kan Sanin Ka’idojin Mu’amula Da Kudade - 3'08"