Kungiyar ECOWAS, ta amince da shirin ficewar kasashe uku da ke karkashin mulkin soji, bayan kusan shekara guda na tattaunawa domin kaucewa wannan bangarewar da ba a taba gani ba a tarihin kungiyar.
“Majalisar ta yanke shawarar sanya wa'adin daga 29 ga Janairu, 2025 zuwa 29 ga Yuli, 2025 a matsayin wa’adin wucin gadi, tare da bude kofofin ECOWAS ga kasashen uku a lokacin wannan wa’adi,” in ji shugaban Hukumar ECOWAS, Omar Touray kamar yadda ya fada a wata sanarwa.
A karon farko cikin kusan shekaru 50 na wanzuwar kungiyar mai mambobin kasashe 15, gwamnatin soji ta Nijar, Mali, da Burkina Faso sun sanar a watan Janairu cewa sun yanke shawarar ficewa daga ECOWAS.
Kungiyar ta cimma wannan matsaya ce a taron da ta yi a Abuja, babban birnin Najeriya a ranar Lahadi.
Gabanin taron, kasashen uku sun amince da ci gaba da barin ‘yan kasashen yankin na ECOWAS su rika shiga kasashensu ba tare da biza ba.
Masu sharhi sun ce ficewar wadannan kasashe uku na iya yin tasiri mai girma kan cinikayya da zirga-zirgar mutane ba tare da wani shinge ko biyan kudi ba, da kuma haɗin kai kan harkokin tsaro a yankin da ƙungiyoyin jihadi ke ci gaba da samun ƙarfi a fadin yankin Sahel.