Jiya laraba a birnin Abuja, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewar har yanzu muradai da walwalar al’ummomin Mali da Nijar da Burkina Faso ne abubuwan da shugabannin ECOWAS ke baiwa fifiko, inda ya bada tabbacin cewa za a yi amfani da hikima da diflomasiya wajen sake zawarcin kasashen cikin kungiyar.
Da yake karbar bakuncin shugaban kasar Jamus, Frank-Walter Steinmeier, dake ziyarar aiki a fadar shugaban Najeriya, Tinubu wanda ya kasance shugaban kungiyar ECOWAS, yace shugabannin kasashen 3 na jan kafa wajen samar da jadawalin mika mulki hannun farar hula da bayanannen lokaci.
Shugaba Tinubu ya shaidawa shugaban na Jamus cewa kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS, za ta bar kofofinta a bude domin dawo da kasashen kan tafarkin dimokiradiya.
“Wannan shi ne matsayar ECOWAS. Koma me yake faruwa a kasashen, mu abin da ya damemu shi ne walwalar al’umma. Bana so in tsawaita batu a matsayina na shugaban ECOWAS. zamu bar kafa domin samun hadin gwiwa,” kamar yadda Shugaba Tinubu ya kara da cewa.
A nasa martanin, shugaban Kasar Jamus yace sake dawo da kasashen 3 cikin kungiyar zai yi matukar tasiri a fannin tattalin arziki da tsaron gabar yammacin Afirka.
Dandalin Mu Tattauna