Musayar wutar jiya laraba a tsakanin sojin dake kokarin maido da shugaban farar hular da aka hambaras bisa karagar mulkin kasar Mali da kuma shugabannin sojin da suka yi juyin mulki, hakan ya sake janyo cikas a kokarin maido da zaman lafiya a kasar Mali. Shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS dake taron kolinsu a birnin Dakar, babban birnin kasar Senegal na tattaunawa kan yadda za’a bullowa wannan matsalar rashin zamana lafiya da juyin mulkin soja ya janyowa kasar Mali.
Makasudin taron kolin yau Alhamis shine a nazarci halin da ake ciki a kasar Guinea-Bisau wadda itama soja sukayi juyin mulki.Amma ganin yadda rikicin Mali yafi kazancewa, shi yasa kungiyar ta ECOWAS ta shigar da batun cikin ajandar tarfon kolin. Darektan ayyukan sadarwa da yada labarai na kungiyar ECOWAS, Sonny Ugoh, ya shaidawa gidan rediyon Amurka cewa taron kolin na fatan ganin kafa Gwamnatin riko karkashin jagorancin farar hula, hakan zai taimaka wajen maido da zaman lafiya a kasar Mali da bada damar shirya sabon zaben. Amma Sonny Ugoh yace wani abin bakin cikin shine kokarin wani juyin mulkin da ya biyo baya a kasar Mali inda aka kashe mutane da dama, haka ya janyo cikas a kokarin maido da zaman lafiya da salon mulkin Demokuradiyya a kasar Mali.