Na shafe shekaru ina neman gurbin karatu a bangaren lafiya kafin na cimma burina bayan an bani wani kwas da ba shi raina ke bukata ba na hakura da karatun a shekara ta, ta farko domin neman abinda nake buri inji wata malamar lafiya Murja Muhammad Aminu.
Na fara karatu ne a bangaren Hotel and catering management, duk da dai ba shi nake shi’awa ba a wannan lokaci, a yayin da nake neman gurbin karatu inji malama Murja
Ta ce tun fara karatunta burinta ta zama ma’aikaciyar lafiya, hakanne ya sa a yanzu ta sake neman gurbin karatu a jamiar Bayero ta Kano.
Ta kuma kara da cewa babban kalubalen da take fuskanta dai shine gwagwarmayar karatu da kananan yara wanda kansu ke ja, inda ta ce ta samu maimaicin aji, amma haka bai sa ta yi kasa a gwiwa ba.
Daga karshe ta yi kira ga ‘ya’ya mata da su jajirce wajan neman ilimi, domin a cewar ta duk mace mai ilimi ta banbanta da sauran mata.
Your browser doesn’t support HTML5