A birnin Lagos, wata kungiya mai suna Women Arise a turance, wadda ke fafutukar kare hakkin bil’adama ta nuna wani majigi dake nuna karuwan cin zarafin bil’adama a Najeriya, da nufin zaburar da gwamnati game da nauyin da ya rataya akan ta na kare hakkin dan'adam.
Dr Ajoke Odumakin ita ce shugabar kungiyar ta Women Arise, ta nanata cewa makasudin nuna wannna majigin shine don fadakar da al’umma cewa ana samun karuwar cin zarafin mata a Najeriya da kuma tauye hakkin bil’adama duk da matakan da hukumomi ke ikirarin dauka, ta ce ya zama dole mu tashi tsaye wajen ankarar da jama’a cewa dukan mu ‘yan uwan juna ne masu neman kare hakkin juna.
Matsalar tauye hakkin bil’adama bai tsaya ga cin zarafin mata ko yara ba, ko yi wa juna rauni, har ma da matakan da hukumomin tsaro ko na shari’a ke dauka na tafiyar Hawainiya wajen bincike da hukunta masu aikata lafuka tare da kwato wa wadanda aka zalunta hakkinsu.
Malam saminu Sha’aibu Jikanshi, na daya daga cikin wadanda suka halarci wannan. Ya yi tsokacin cewa shima ya na daya daga cikin wadanda aka tauye wa hakki a lokacin da wani ya damfareshi amma har yanzu babu abin da jami’an tsaro ko hukumar EFCC suka yi duk da cewa sun san da zancen.
Rahotanni sun nuna cewa mata da yara sune aka fi tauye wa hakkinsu musmman ta yi masu fyade. Wata Uwa da aka sakaya sunanta ita ma ta koka akan yadda aka yi wa diyar ta fyade, duk da cewa wannan koken na gaban wata kotu a jihar Ogun, amma ana tafiyar hawainiya wajen gudanar da shari’ar.
Dr. Ajoke ta kara da cewa suna sane da tafiyar hawainiyyar da jami’an tsaro da hukumomi ke yi, duk dai hakan zai taimaka wajen kaucewa hukunta wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Amma akwai bukatar ganin an gudanar bincike da shari’u cikin hanzari don hakan ya zama darasi ga masu aikata laifuka irin wadannan.
Ga karin bayani daga Babangida Jibirin.
Your browser doesn’t support HTML5