Dubban Maniyatan Jamhuriyar Nijer Sun Shiga Halin Zullumi

Alhazai A Saudiyya

Yayinda har yanzu kashi 2 daga cikin 3 na maniyatan hajin bana ke jiran zuwan jiragen da zasu kwashe su don zuwa kasa mai tsarki hukumomi sun bada tabbacin daukan dukkan matakan da zasu ba alhazan damar safka kasar Saudia kafin wa’adin rufe filayen jiragen saman Madina da na Jidda ya cika.

Har I zuwa ranar laraba maniyatan Nijer 2000 kacal ne suka safka kasar Saudiya daga cikin 7194 da suka samu rajistar hukumar alhazai, Wannan ya sa wasu daga cikin ejoji da maniyata dukansu mata suka yi tattaki domin kai koke a ofishin fra minista dake nan yamai.

Faruwar wannan al’amari ya sa hukumomi fitar da sanarwa inda suka yi kira a kwantar da hankali domin a cewarsu sun dauki matakan kawo karshen tsaikon da aka fuskanta a ayyukan jigilar alhazai. Ministan bunkasa kiwon dabobi Tidjani Aboulkadri shine kakakin gwamnati.

Baya ga matsalar jiragen dakon alhazai wata matsalar ta daban da ake dauka a matsayin dalilan da suka haddasa jwannan inkiri matsala ce ta rashin samun Visa.

A ranar 3 ga watan yulin dake tafe ne ake rufe filin jirgin saman Medina yayinda za a dakatar da safka da tashin jiragen a filin jirgin Jidda a ranar 6 ga watan na Yuli lamarin da ya jefa maniyatan Nijer cikin halin zullumi inda a yau wadanda suka fito daga jihohi ke cika mako kusan 2 a yamai suna jiran zuwan jirgin da zai kai su kasa mai tsarki abinda ke nufin galibinsu sun cinye rabin guzuri tun a nan gida.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Dubban Maniyatan Nijer Sun Shiga Halin Zullumi