Danald Trump yana zargin ta da amfani da bakaken fatar Amurka kawai saboda kuri’arsu, yayin da take nuna rashin kulawa da rashin ayyukan yi wanda ke jefasu cikin aikata manyan laifuka.
Trump ya dade yana gayawa bakar fatar Amurka cewa shekaru masu yawa gwamnatin jam’iyyar Democrat ta yi watsi da su, yana kuma tambayarsu cewa me zasu rasa idan suka zabi jam’iyyar Republican a watan Nuwamba.
Bayan kwashe ‘yan kwanaki yana irin wadannan kalamai ne, Clinton ta mayar da martani ga Trump a jiya Alhamis.
A lokacin da take magana a jihar Nevada, Clinton tace Trump yana amfani da kalamai irin na cin zarafi da rashin ilimi ga bakaken fata, yana kallonsu ne kawai a matsayin wadanda suka gaza,
Tace wannan abin takaici ne domin Trump baya ganin irin ci gaban da aka samu, irin na masu kasuwanci da wadanda suka kammala karatunsu daga makarantun bakake, da yadda Majami’ai ke taka rawa a rayukansu.
Clinton ta lura da cewa ma’aikatar Shari’ar Amurka ta yi 'karan Trump, a dalilin zarginsa da akayi na nuna banbanci wajen bayar da hayar gidaje ga bakaken fata da kuma Hispaniyawa, haka kuma Trump shine ya yi ta cewa an haifi shugaba Obama a kasar Kenya, maimakon ya amince da bakar fata a matsayin shugaban kasarsa.