Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Laraba Mataimakin Shugaban Amurka Ya Isa Kasar Turkiya


Joe Biden Mataimakin Shugaban Kasar Turkiya
Joe Biden Mataimakin Shugaban Kasar Turkiya

Yau Laraba ake sa ran mataimakin shugaban Amurka Joe Biden zai isa Turkiyya, a kuma yau din ne dakarun kasar suka kaddamar da hari na farko cikin Syria, inda suka auna mayakan sakai na ISIS da kuma 'yan tawayen kurdawa.

Haka nan Mr. Biden yana isa kasar a kuma dai dai lokacinda jiragen yakin Amurka suka tallafawa kutsen da sojojin Turkiy ya yi cikin Syria. Mataimakin shugaban na Amurka tareda PM kasar Binali Yildrim zasu yi taro na hadin guiwa da manema labarai, bayan da ya gana da manayan jami'an kasar ciki harda shugaban kasar Rajib Tayyib Ergodan., a Ankara babban birnin kasar.

Mr. Biden shine wani babban jami'i a gwamnatin Obama kuma na hanun damansa, wand a galibi yake wakiltar fadar White House a harkokin difilomasiyya masu sarkakiya. Mataimakin shugaban kasar yayi suna wajen kulla dangantaka d a shugabannin kasashen duniya, ciki harda Erdogan, mutumin d Biden ya kira "dadadden abokinsa."

Joe Biden da Firayim Ministan Turkiya
Joe Biden da Firayim Ministan Turkiya

Yau Laraba, Erdogan ya sake nanata kira ga Amurka ta mika kasar malamin addinin Islaman nan dan kasar Fethullah Gulen wanda yake da zama anan Amurka dangane da zargin da kasar take yi masa cewa yana da hanu a yunkurin juyin mulkin da aka so ayi kasar wanda bai sami nasara ba. Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fada jiya Talata cewa ta sami bukatar da Turkiyya ta gabatar na neman a mika mata malamin dan shekaru 75 d a haifuwa, amma bukatar bata fito fili ta nuna shaida irin rawar da Gulen ya taka a yunkurin juyin mulkin.

Jami'an ma'aikatar shari'a ta Amurka tace za'a yanek shawarar kan batun mika malamain ne tareda la'akari da shaidar da aka gabatar, da kuma irin sharuddan da suke kunshe cikin yarjejeniyr mikawa juna mutane da kasashen suke nema.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG