Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Joe Biden: Amurka A shirye Take Domin Sauraron Duk Wata Shaida Daga Turkiyya Kafin Ta Yanke Hukunci


Mataimakin Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce Fadar Shugaban Kasar Amurka ta kuduri aniyar sauraron duk wata shaidar da Turkiyya ta iya gabatarwa, kafin ta yanke shawarar ko za ta mika ma ta Malamin addinin Musuluncin nan mai suna Fethullah Gulen.

Gulen dai na zaune ne a jahar Pennsylvania da ke gabashin Amurka, kuma Turkiyya na bukatar a mika ma ta shi ba tare da bata lokaci ba, ta na mai zarginsa da shirya juyin mulkin nan na watan jiya wanda bai yi nasara ba -- zargin da Malamin ya karyata.

Biden ya gana jiya Labara da Shugaban Turkiyya Raccep Tayyip Erdogan. Ya yi kokarin sanya Erdogan ya sassauto game da nuna rashin hakurinsa, ta wajen bayyana yadda kotunan Amurka kan bukaci kwararan hujjoji, kafin a mika ma wata kasa mutumin da ta ke zargi.

Ya ce masu gabatar da kara na bukatar su nuna ma alkali abubuwan ka iya zama dalilan aukuwar al'amari, kuma wani sa'in kotunan kan bi a hankali. Biden ya yi nuni da yiwuwar a tsige Shugaba Barack Obama, muddun ya ba da umurnin tasa keyar wani dan kasar waje ba tare bin cikakken ba'asi ba.

Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya ce muddun aka bata lokaci wajen tasa keyar Gulen zuwa Turkiyya, to dangantakar Amurka da Turkiyya fa za ta yi tsami.

Biden ya ce ya fahinci bacin ran Turkiyya, ya kuma kara da cewa Amurka fa ba ta da wata niyya ta kare duk wani mutumin da ya yi wani abin da ka iya lahani ga kawarta.


v

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG