Dole Ne 'Yan Sanda Su Sake Salo Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga: IGP

Rundunar ‘yan Sandan Najeriya ta ce dole ne ta fito da sabbin dabaru da zasu kai ga dakile ayyukan mahara da na ‘yan ta’adda a kasar.

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya (IGP) Muhammad Adamu ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke jawabi ga manyan hafsohin rundunar a shelkwatar ‘yan sanda da ke jihar Katsina.

A jawabin da ya yi wa manyan hafsoshin ‘yan sandan, Adamu ya ce harkar tsaron cikin gida aiki ne na ‘yan sanda kuma ya zama wajibi a garesu su zage damtse wajen ganin cewa an murkushe tare da dakile ayyukan ta’addanci.

Ya kara da cewa a ‘yan kwanakin nan sun lura cewa akasarin ayyukan ta’addanci da ake yi sun karkata ne zuwa yankin arewa maso yammacin Najeriya, ya ce ba zasu lamunci hakan ba.

Ya kuma ce a kokarin da suke yi na ganin sun cimma burinsu na tsaro, ya zama wajibi su sake salo tare da dabarun yaki da ayyukan ta’addanci, da hada hannu da dukkanin rundunonin tsaro a fadin tarayyar Najeriya.

Sufeto Janar Muhammad ya kara da cewa ya kamata ‘yan sanda su hada hannu da irinsu kungiyar makiyaya ta Myetti Allah wadanda suka san lungu da sako na dazuzzukan da ke cikin Najeriya, ya na mai cewa ta wannan hanyar ne kawai ‘yan sanda zasu samu nasarar fatattakar ‘yan ta’adda tare da hana su matsugunin da suke kitsa ayyukan ta’addanci a yankin.

Karin bayani akan: sojojin Najeriya​, sojoji, Muhammad Adamu​, da Nigeria.

Your browser doesn’t support HTML5

Dole Ne 'Yan Sanda Su Sake Salo Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga: IGP


Karin bayani akan: sojojin Najeriya​, sojoji, Muhammad Adamu​, da Nigeria.